Ana Wata: Gwamnatin Kano Tayi Rinton Aikin Ginin Asibitin KAFIN MAIYAKI – In Ji Shugaban APC

FB IMG 1719582014353

Muna janyo hankalin al’ummar wannan Jiha da suyi watsi da wannan farfaganda ta rinton aiki da jami’an gwamnatin Nnpp suka fitar akan samar da wannan asibiti.

Alfijir labarai ta ruwaito shugabancin Jam’iyyar Apc na Karamar Hukumar Kiru Aminu Alhassan Kiru yace, a  madadin kafatanin ‘yan Jam’iyyar muna sanar da duniya cewa labarin da ake yadawa cewar gwamnatin Nnpp ta Jihar Kano ta gina da samar da kayan aikin asibiti a garin Kafin Maiyaki ba gaskiya bane, rinton aiki ne da suka saba.

Wannan asibiti na garin Kafin Maiyaki, gwamnatin Apc karkashin mulkin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ce ta gina shi a zamaninsa tare da samar da dukkan kayayyakin da yake bukata don samar da ingantaccen kulawa ga al’ummar wannan yanki.

Muna janyo hankalin al’ummar wannan Jiha da suyi watsi da wannan farfaganda ta rinton aiki da jami’an gwamnatin Nnpp suka fitar akan samar da wannan asibiti musamman saboda hujjojin da zamu gabatar a wannan rubutu.

Bayan ayyukan gini da gwamnatin Jihar Kano ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta samar, akwai dakin kwanciya sabo wanda tsohon dan majalisar tarayya na Apc Hon. Aliyu Datti Yako ya gina a wannan asibiti tsakanin 2019 – 2023 kamar yadda ake iya gani a cikin hotunan.

Wannan aikin gini an fara shine a zangon farko na gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje (2015 – 2019) wanda aka baiwa kamfani mai suna Maiyaki Integrated Links Limited.

Bayan kammala aikin ginin da gwamnatin tayi, an sake baiwa kamfanin Maiyaki Integrated Links  Limited kwangilar sayo kayayyakin amfani a wannan asibiti akan kudi N132, 763, 047:49 kamar yadda yake kunshe a takarda mai lamba MOH/SMTB/001/2020/I/23  ta ranar 7/1/2021 kamar yadda yake a rubuce a jikin takardar dake hade da wannan rubutun.

Domin sake tabbatar da karyar da sukayi, mun tanadi hotuna na bikin karbar kayan asibitin da akayi ranar 24/5/2023 da kuma bikin kaddamar da kayan asibitin da aka kawo wanda Shugaban Karamar Hukumar Kiru ya jagoranta ranar 27/5/2023  wanda har Mai girma Hakimin Kiru, Dan madamin Karaye ya halacci wajen wannan taro.

Dangane da wadannan hujjoji da muka gabatar, muna janyo hankalin mutanen wannan jiha da suyi watsi da wannan farfaganda da gwamnatin Jiha  take yadawa cewa ita ta samar da wannan asibiti da kayan aiki a garin Kafin Maiyak,i kuma muna basu shawara akan su daina rinton ayyukan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi su tsaya su daina kirkirar rigingimun siyasa da yake hanasu nutsuwa suka kasa yiwa al’ummar Jihar Kano ayyukan raya kasa.

Mu al’ummar wannan karamar hukuma ta Kiru ba timawa bane, munsan wanda yayi mana aiki kuma tuntuni mun riga munyi masa godiya.

IMG 20240628 WA0534
Kiru
IMG 20240628 WA0535
Kiru

Aminu Alhassan Kiru
Shugaban Jam’iyyar Apc
Karamar Hukumar Kiru

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *