Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP ta ce Gwamna Abbah Yusuf na Jihar Kano zai ci gaba da kasancewa a dakace har zuwa watan Disamban wannan shekarar.
Alfijir labarai ta ruwaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren jam’iyyar na kasa Mista Oginni Olaposi Sunday ya fitar a Abuja.
A cewar sanarwar, Jam’iyyar za ta gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki a Babban Birnin Tarayya Abuja a karshen wannan wata domin magance matsalolin cikin gida da suka shafi Jam’iyyar, inda ta ƙara da cewa ana sa ran dukkan Shugabannin Jam’iyyar da dattawa a fadin kasar za su halarci taron.
Sunday ya bayyana cewa za a tattauna muhimman batutuwan da suka shafi Jam’iyyar tare da daukar kwararan matakai don ƙara jaddada dakatarwar ɗan Takararta na Shugaban ƙasa a zaben 2023 Dr. Rabi’u Kwankwaso, da Buba Galadima da ɗaukacin kwamitin Jagorancin Jam’iyyar na ƙasa karkashin jagorancin Dr. Ahmed Ajuji.
Ya kuma bayyana cewa taron masu ruwa da tsaki na da matukar muhimmanci ga Shugabancin jam’iyyar NNPP domin ci gaban dimokradiyya da ci gaban jam’iyyar gabanin zaben 2027 mai zuwa.
Haƙiƙanin jajircewa na duka masu ruwa da tsaki ta bangaren ƙwazo da maida hankali zai kasance da fa’ida sosai ga nasarar taron.
An wajabta wa dukkan mambobi musamman wadanda ke rike da mukamai masu muhimmanci da su halarci wannan taro mai zuwa.
Ya kamata dukkan zababbun mambobin jam’iyyar NNPP su fahimci illar yin zagon ƙasa ga Jam’iyya gabanin zaben 2027 musamman kuma idan ba su halarci taron ba.
Kuma za a iya cewa Kwankwaso, da Buba Galadima da ɗaukacin mambobin tsohon kwamitin ayyuka na kasa karkashin jagorancin Dr. Ahmed Ajuji na ci gaba da kasancewa a dakace a jam’iyyar ta NNPP.
“Haka kuma Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf shima zai ci gaba da kasancewa a dakace har zuwa watan Disamba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, fatanmu shi ne INEC za ta ɗauki nauyin mutunta jigon dimokuradiyyar cikin gida da manufofin ci gaba don dorewar dimokuradiyya a Najeriya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj