Ana Wata: Kotu ta cire shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso daga muƙamin sa

FB IMG 1760790928482

Babbar Kotun Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Abdu Mai Wada Abubakar ta yanke hukuncin tube Abdullahi Basaf daga mukaminsa na shugaban karamar hukumar Kumbotso, tare da bayyana Ali Musa “Hard Worker” a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben.

Kotun ta kuma umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSEIC) da ta janye takardar shaidar nasarar da ta bai wa Abdullahi Basaf, tare da mika ta ga Ali Musa ba tare da bata lokaci ba.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman kotun a ranar Talata, lauyan Ali Musa, Jazuli Mustafha, ya bayyana cewa tun a shekarar 2024 suka shigar da kara kan jam’iyyar NNPP da KANSEIC da kuma Abdullahi Basaf. Ya ce karar ta shafi sauya sunan wanda yake karewa a matsayin halastaccen dan takarar shugabancin karamar hukumar Kumbotso.

A cewarsa, a wani hukunci da Mai Shari’a Usman Naabba ya yanke a baya, an tabbatar da Ali Musa a matsayin sahihin dan takara, tare da umartar NNPP da KANSEIC su amince da shi. Sai dai duk da wannan umarni, ba a aiwatar da shi ba, inda aka ci gaba da gudanar da zaben ba tare da bin umarnin kotu ba.

“Duk da hukuncin da kotu ta yanke a baya, an gudanar da zabe kuma aka rantsar da wanda kotu ba ta amince da shi ba,” in ji Mustafha.

Ya kara da cewa sabon hukuncin da kotun ta yanke a yanzu ya amince da dukkan bukatunsu, inda ta soke takardar shaidar nasarar da aka bai wa Basaf, ta cire shi daga mukaminsa, sannan ta umurci KANSEIC da ta amince da Ali Musa tare da rantsar da shi nan take a matsayin zababben shugaban karamar hukumar Kumbotso.

“A wannan karo, kotu ta gyara abin da bai dace ba a baya, ta soke rantsar da Basaf, tare da umartar a rantsar da wanda muke karewa ba tare da bata lokaci ba,” in ji shi.

Sai dai a bangaren lauyan Abdullahi Basaf, ya ki cewa komai lokacin da manema labarai suka tuntube shi domin jin ta bakinsa bayan yanke hukuncin.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *