Wata babbar kotun jihar Osun da ke zamanta a Ede ta tasa keyar wani basarake, Elegbedi na Egbedi a jihar Osun, Oba Muideen Azeez da wasu mutane hudu da ake tuhuma a gidan yari na Ile-Ife.
Alfijir labarai ta rawaito ana ci gaba da tsare wadanda ake tuhumar ne a ranar Alhamis sakamakon kasa cika sharuddan belin da kotu ta bayar.
Sarkin da sauran wadanda ake tuhuma sun gurfana a gaban kotu bisa zargin kone-kone da barna a wata gona a garin Iloba.
Akibu Abioye, Yisa Akolapo, Rasidi Ayandiran da Sarafadeen Abioye, su ne sauran wadanda ake tuhuma da ke zaman shari’a tare da sarkin a gaban kotun bisa tuhumar tuhume-tuhume 29.
Mai shari’a Kudirat Akano a ci gaba da zaman shari’ar a ranar Alhamis ta bayar da belin wadanda ake kara a kan kudi N5m tare da tsayayyu biyu kowannen su.
Daya daga cikin wadanda za su tsaya masa, mai shari’a Akano ta bayyana cewa, dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnati mai mataki na 16 da ke da kadarorin da ke karkashin ikon kotun.
Daily Post
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj