Ana Wata: Masu Unguwanni 13 Sun Yi Murabus daga Mukamansu a Jihar Kano.

best seller i

Wasu Masu Unguwanni 13 Sun Yi Murabus daga Mukamansu a Jihar Kano.

Hakimin gundumar Jogana da ke ƙaramar hukumar Gezawa, Alhaji Abdulkadir Muhammad Balarabe, ya tabbatar da murabus ɗin masu unguwanni 13 a ƙasarsa, waɗanda suka sauka daga mukamansu bisa ga ra’ayinsu na kansu.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Jogana, ranar Talata 2 ga Satumba, 2025, hakimin ya bayyana cewa:

“Masu unguwannin da suka yi murabus duk sun sanya hannu a takarda. Sun bayyana cewa idan aka hukunta wani mai unguwa da aka kai ƙara kansa kan zaluntar jama’a, to su ma za su sauka daga kan mukamansu. Bayan hukuncin da aka yanke masa, sai suka mika murabus ɗinsu.”

A nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Gezawa, Hon. Mukaddas Bala, ya yi godiya ga hakimin gundumar Jogana bisa jajircewarsa wajen tabbatar da gaskiya da adalci, ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su zauna lafiya da juna.

Hakimin Jogana, Abdulkadir Muhammad Balarabe, ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a naɗa sababbin masu unguwanni da za su maye gurbin waɗanda suka sauka.

ABK News

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *