Majalisar dokokin jihar Kano ta fada cikin rudani lokacin da kakakin majalisar Jibril Isma’il Falgore ya kirawo tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa.
Alfijir labarai ta ruwaito kakakin majalisar na cewa Ganduje shugaban rikon jam’iyyar APC ne a lokacin da yake mika sakon ta’aziyya ga uwargidansa Farfesa Hafsat Ganduje kan rasuwar mahaifiyarta, wanda ya haifar da zazzafar muhawara.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar Labaran Abdul Madari da wasu ‘yan majalisar APC ne suka fito da batun, inda suka ce yanzu Ganduje ne cikakken shugaban jam’iyyar APC na kasa ba shugaban riko ba ne.
Daga bisani majalisar ta dage zaman har zuwa ranar Talata.
A wannan rana ce dai majalisar dokokin jihar Kanon ta dawo zama tun bayan hutun kwanaki 48 da ta yi, wanda ta tafi bayan zartar da kudirin dokar soke masarautu biyar na jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa an majalisar ta jinkirta komawa bakin aikinta ne saboda matsalar tsaro da ta taso bayan rushe masarautun.
Nigerian Tracker
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj