Daga Aminu Bala Madobi
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kori Solomon Arase daga mukaminsa na shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC).
Alfijir labarai ta ruwaito Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa, Tinubu ya ce shugaban ya kuma amince da nadin DIG Hashimu Argungu (Rtd) a matsayin sabon shugaban hukumar.
“Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin DIG Hashimu Argungu (Rtd) a matsayin sabon shugaban hukumar ‘yan sanda (PSC).
“Shugaban ya kuma amince da nadin Cif Onyemuche Nnamani a matsayin Sakatare da DIG Taiwo Lakanu (Rtd) a matsayin mamba a hukumar.
“Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin. Za a nada sauran mambobin hukumar kula da aikin ‘yan sanda a wani dan lokaci na daban.
“Bugu da kari, shugaban kasa ya amince da nadin Mista Mohammed Sheidu a matsayin babban sakataren asusun kula da ‘yan sandan Najeriya (NPTF).
“Shugaban kasa yana bukatar nuna gaskiya, himma, da kishin kasa wajen gudanar da wadannan muhimman ayyuka don kyautata rayuwar ‘yan sandan Najeriya da kasa baki daya.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj