Ibtila”i! Dakarun Boko Haram Sun Sace Fasinjoji A Hanyar Maiduguri Zuwa Kano

FB IMG 1718099197879

Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan ta’addan sun kai hari ne a tsakanin Garin Kuturu da kauyen Mannari da ke kusa da Auno, wanda ke kan hanyar Damaturu da misalin karfe 5:50 na yammacin Jiya Litinin.

Alfijir labarai ta ruwaito rahotanni sun ce sun tare babbar hanyar kafin su kwashe wasu fasinjoji da karfin tsiya su tafi dansu.

Lamarin da ya sa daruruwan matafiya da masu ababen hawa suka makale a sassan biyu na hanyar da ta kasance mai yawan hada-hada.

Mazauna yankin sun ba da labarin yadda direbobin ‘yan kasuwa da yawa suka fake a cikin al’ummarsu na Ɗan lokaci lokacin da maharan ke Gudanar da ayyukansu a Tsakanin kauyukan Garin Kuturu da Mannari.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *