Ana Zaton Wuta A Makera: An Kama Rijistaran Kuɗi na kotun Musulunci Kan Zargin Saka Miliyan 35 na Marayu a Crypto

FB IMG 1760198620995

Babban magatakardar kotunan, Alhaji Abubakar Haruna Khalil, ne ya tabbatar da hakan a yayin da ya zanta da Premier Radio, inda ya ce hukumar na gudanar da bincike ne domin tabbatar da gaskiyar zarge-zargen.

Haka kuma, Alhaji Khalil ya ce duk wasu matakai da za a ɗauka za su kasance cikin bin doka da oda, domin kare hakkokin marayu da tabbatar da gaskiya a harkokin kotunan Musulunci.

Binciken ya biyo bayan rahotannin da ke nuna almundahana da amfani da kudaden jama’a a harkokin saka jari marasa izini, lamarin da ya janyo hankalin hukumar kula da kotunan ɗaukaka kara.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *