ASUU Ta Koka Da Cin Zarafi Da Korar Mambobinta A Jami’o’i

ASUU

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, ASUU ta koka kan cin zarafi da matsantawa da ake yi wa mambobinta a wasu jami’o’in gwamnati.

Alfijir Labarai ta rawaito hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da ko-odinetan kungiyar, shiyyar Kano, Abdulkadir Mohammed ya fitar a yau Asabar .

Ya bada shaida kan kin bin matakan da aka tanada da kuma kin biyayya ga dokokin da su ka kafa jami’a a Nijeriya.

Ya bayyana damuwa kan batun, inda ya yi bayanin cewa hukumomin gudanarwa da gwamnoni basa abinda ya dace game da tafiyar da jami’o’i.

Mohammed ya bayyana sunayen jami’o’in Kogi da Legas da Ebonyi da AAU a matsayin inda ke zargin samun matsalolin.

Sauran, ya ce akwai jami’ar fasaha ta Owerri da jami’ar COOU inda mambobin ASUU ke fuskantar kalubale.

A kayyade, ya bayyana yadda aka kori mambobi 120 na ASUU daga jami’ar KSU tun daga 2017 kawai saboda neman samar da walwalar aiki.

“Akwai korar da aka yi wa shugaban ASUU na LASU ba bisa ka’ida ba da mataimakin sa a 2017 saboda sun dage kan abi ka’ida.”

Mohammed ya ce ASUU za ta bi dukkan matakan shari’a wajen ganin an dawo da mambobin da aka kora.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *