Atiku, Kwankwaso Da Peter Obi Sune Suka Haifar da tsadar Rayuwa Da Hauhawar farashin kayayyaki – Inji Shettima

IMG 20240221 080353

Yan Siyasar da Suka fadi A Zaɓen 2023 irinsu Atiku Abubakar da Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi Sune Suka Haifar da tsadar Rayuwa, Hauhawar farashin kayayyaki: Inji Shettima

Alfijir labarai ta rawaito mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya zargi ‘yan siyasar da suka sha kaye a zaben 2023 da yunkurin jefa Najeriya cikin rikici, tare da yiwa kasar zagon kasa ta hanyar safarar abinci zuwa wasu kasashe domin tayar da farashin kayan abinci.

Shettima ya bayyana haka ne a jiya Talata, a wani taro kan harkokin kula da dukiyar jama’a a Abuja, ya yi ikirarin cewa an kama manyan motoci 45 da ke safarar abinci daga kasar Zuwa Wasu ƙasashe.

Shattima ya jaddada cewa wasu ’yan siyasa na shirin jefa Najeriya cikin rikici saboda Gazawar da suka yi na kwace mulki a zaben da ya gabata.

Sai dai Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party da Peter Obi na jam’iyyar Labour, Manyan ‘yan takara a babban zaben, sun ci gaba da nuna rashin amincewa da yadda Tinubu ke tafiyar da tattalin arzikin ƙasar.

Duk da cewa an samu karin farashin kayan abinci kafin Gwamnatin Tinubu, kwatsam Cire tallafin man fetur da yayi ya sanya farashin man fetur ya tashi daga N145 zuwa N630, lamarin da ya yi tashin gwauron zabin abinci yayin da Naira ke ci gaba da faduwa a kan Dala, inda aka sayar da ita a kan N1,825. dala a ranar Talata.

Tinubu, Yayi martani ga koke-koke da jama’a suke yi kan tsadar kayan abinci da hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan, ya umurci ma’aikatar noma da samar da abinci da ta saki kimanin tan metric ton 42,000 na hatsi da suka hada da masara, gero Shinkafa Domin kawo sauki ga al’ummar ƙasar

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *