Ya Kamata Hukumar Kwastam Ta Sakar Wa ’Yan Kasuwa Mara — Sarkin Kano

IMG 20240221 082110

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya shawarci Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa da ta ƙyale ’yan kasuwa su riƙa gudanar da harkokin kasuwancin su ba tare da tsare musu kayansu ba matuƙar ba su karya doka ba.

Alfijir labarai ta rawaito wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwar ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Sakataren yada labarai na Masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa.

Sarkin ya yi wannan kira ne a yayin da ya karɓi bakuncin Mataimakiyar Babban Kwamandan Kwastam na Kasa mai kula da shiyyar Kano, Katsina, Kaduna da Jigawa, Queen Ogbudu da tawagarta a fadarsa.

Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya bayyana cewa a baya jami’an Hukumar Kwastam suna shiga kasuwanni su karɓe wa ’yan kasuwa kaya ba bisa ka’ida ba, amma yanzu ya ji daɗi da hakan ya zama tarihi.

Haka kuma, Sarkin ya shawarci Hukumar Kwastam da ta zauna da ’yan kasuwa domin wayar musu da kai kan irin kayan da hukumar suke so a shigo da su domin ci gaban kasa da kuma al’umma baki ɗaya.

A nata jawabin, Queen Ogbudu ta ce ta ziyarci Kano ne domin sanar da Sarkin cewa Shugaban Kasa ya ba da umarni da su fitar da kayan abinci domin raba wa al’ummar kasa la’akari da matsin da ake fama da shi.

Kazalika, Sarki Aminu ya karɓi bakuncin tawagar mutanen kasar China karkashin jagorancin Mista Lee Zhong, sai kuma bakuncin Shugaban Kwalejin Aikin Gona ta Kasa da ke Kano, Dokta Muhammad Yusha’u Gwaram a fadarsa.

Za mu raba wa ’yan Najeriya kayan abinci — Kwastam

Aminiya ta ruwaito cewa, a wannan Talatar ce Hukumar Kwastam ta Najeriya, NCS, ta ce tana shirin raba wasu kayayyakin abincin da aka kama a faɗin ƙasar, yayin da ake ci gaba da fama da matsalar karancin abinci a kasar.

A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar, CSC Abdullahi Maiwada, za a raba kayan abincin ne bayan an tabbatar da cewa mutane za su iya amfani da su.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an ɗauki matakin ne “domin rage wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta da kuma inganta hanyoyin samun kayan abinci, hukumar kwastam za ta taimaka wajen raba kayan abincin da hukumar ta kama kai tsaye.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Za a sanar da tsarin da za a yi amfani da shi a ofisoshin hukumar da ke fadin kasar, tare da jajircewa wajen tabbatar da adalci.

“Mun sha alwashin cewa za a gudanar da wannan aikin domin tabbatar da cewa kayayyakin sun kai ga waɗanda suka fi bukata.”

FB IMG 1708499921679
📸 Masarautar Kano
FB IMG 1708499941572
📸 Masarautar Kano

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *