Alfijr ta rawaito Fitaccen mawaƙin nan Naziru M. Ahmad wanda ake yi wa laƙabi da Sarkin Waƙa, ya bayyana cewar, ba bukatar talaka ce ta kai su ba, matsalar su ce ta zaɓe, wanda a tunanin su idan an ɗaga za su ci zaɓe.

Sarkin waƙa ya bayyana cewa “yanzu har akwai wani Gwamna wanda zai ce maka sai yanzu ne yake jin tausayin talaka?
Lokacin farkon mulkinsu wanne irin abu ne ba su yi wa talaka ba?
Ya ƙara cewa, an yi lokacin korona, babu malamin da ya iyi kira akan su sassautawa talaka ba,
Hakazalika idan an ba su abinci da kuɗi a lokacin korona ɓoyewa suke, duk a wannan lokacin ba su ji tausayin talaka ba?
An kashe mutane duk ba su je gurin shugaba Buhari ba sai yanzu domin buƙatar kujerunsu.
Rariya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇