“Ba Tinubu bane ke shugabantar ƙasar mu ba, Trump ne ke mana mulkin mallaka” — Naja’atu ga Tinubu

IMG 153710 301225 1767105466206

Daga Aminu Bala Madobi

Fitacciyar ‘yar gwagwarmayar siyasa, Hajia Naja’atu Mohammed, ta fito fili ta bayyana ra’ayinta mai zafi kan halin da Najeriya ke ciki, tana zargin cewa ƙasar ta sake faɗawa sabon tsarin mulkin mallaka na ƙasashen yamma.

A cewarta, Bola Ahmed Tinubu ba shi ne shugaban Najeriya a aikace ba, inda ta ce Donald Trump ne “sabon shugaban Najeriya” ta fuskar tasirin siyasa da tattalin arziƙi.

Naja’atu ta yi ikirarin cewa haraji da dukiyoyin Najeriya na tafiya hannun ƙasashen waje, ciki har da France, tana mai cewa an mayar da ƙasar tamkar kasuwanci ne kawai.

“Ba za mu yarda da wannan ba,” in ji ta, tana kira ga ‘yan Najeriya da su farka su ƙi duk wani yunƙuri na tauye ‘yancin ƙasa da ikon mulki.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *