Ba Za Mu Biya Ƴan Bindiga Ko Sisin Kwabo Ba – In Ji Shugaba Tinubu

Screenshot 20240307 214501 com.android.chrome edit 1362016366979

Shugaban Kasar Najeriya Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro kada su biya kuɗin fansar sakin kusan ɗalibai 300 da malaminsu da aka yi garkuwa da su makon da ya gabata daga wata makaranta da ke Kaduna.

Alfijir labarai ta rawaito Tinubu ya kuma umarci hukumomin tsaro su tabbatar an kuɓutar da dukkan mutanen da aka sace ba tare da biyan ƴan bindigar kuɗin fansa ba, kamar yadda ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris ya shaida wa ƴanjarida a ranar Laraba.

Ministan ya ce shugaba Tinubu ya faɗa wa sojojin da ke laluben inda ɗaliban suke su tabbatar “ba a biya ko sisin kwabo ba”.

Tun farko, ƴan’uwan ɗaliban da ke tsaren sun ce ƴanbindiga sun buƙaci a biya su kuɗi mai yawa domin su saki yaran da suka sace daga makarantarsu a ƙauyen Kuriga.

Cikin makon da ya gabata, an sace mutane da dama ciki har da fiye da mutum 60 daga wani ƙauye a dai jihar ta Kaduna.

Cikin shekara uku da ta gabata, ɗaruruwan ɗalibai aka sace. Wasu a cikinsu an sake su bayan tattaunawa da hukumomi duk da cewa jami’ai sun musanta biyan kuɗin fansa.

Wata doka da aka amince da ita a 2022 ta hana biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *