Ba za mu iya biyan mafi ƙanƙantar albashi na N60,000 ba -In ji Gwamnonin Najeriya

IMG 20240608 WA0001

Gwamnonin Najeriya 36 sun yi watsi da naira 60,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi da gwamnatin tarayya ta ce za ta biya ma’aikatan ƙasar tun da farko.

Alfijir labarai ta rawaito cikin wata sanarwa da ƙungiyar gwamnonin ƙasar, ta wallafa a shainta na X, sun ce biyan 60,000 a matsayin mafai ƙarancin albashi ba abu ne da zai ɗore ba.

”Kenan hakan na nufin da yawa daga cikin jihohin za su riƙa kashe duka kuɗin kason da suke samu daga gwamnatin tarayya wajen biyan albashin ma’aikata, ba tare da komai ya ragu ba don gudanar da wasu ayyuka”, in ji sanarwar.

Gwamnonin sun ce daga ƙarshe wasu jihohin za su ƙare da cin bashi don biyan ma’aikata a kowane wata.

”Wannan ba abu ne da zai amfani ƙasarmu ba, ciki har da ma’aikata”, in ji gwamnonin.

A ranar Talata 4 ga watan Yuni ne ƙungiyar ƙwadago ta janye yajin aikin da ta fara a farkon makon bayan wata ganawa da wakilan gwamnatin tarayya.

Gwamnatin tarayyar dai ta alƙawarta biyan sama da naira 60,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashin.

Ƙungiyoyin ƙwadagon dai sun buƙaci gwamnatin tarayya ta biya naira 494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.

To sai dai gwamnonin ƙasar sun yi kira ga duka ɓangarorin biyu, musamman ƙungiyoyin ƙwadago su yi la’akari da halin tattalin arziki da ƙasar ke ciki wajen amincewa da abin da za a iya ci gaba da biya, da zai daɗaɗa wa duka ɓangarorin biyu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *