Iyalan marigayi Janar Mamman Jiya Vatsa, wanda aka kashe a shekarar 1986 bisa zargin yunkurin juyin mulki kan tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida (IBB), sun bayyana littafin tarihin da Babangida ya fitar kwanan nan a matsayin littafi mai “cike da karya da karkatar da gaskiya” da kuma “kyakkyawan littafi na tunani ga ‘yan ta’adda”.
Jonathan Vatsa, wanda ke magana da yawun iyalan Vatsa kuma ɗan uwan marigayin, ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a Minna ranar Talata cewa sun fusata da yadda Babangida ke kare kisan Vatsa da hujjar cewa an same shi da laifi a yunkurin juyin mulki.
“Babangida Ya Rasa Daraja Saboda Karya da Rashin Adalci” da yayi a littafinsa.
A cewar Jonathan Vatsa:
“Janar Babangida mutum ne da ya rasa mutunci da daraja saboda yawancin karya da ya rubuta a cikin wannan littafin tarihin da ya fitar a kurarren lokaci.”
Ya kara da cewa:
“Littafin Babangida cike yake da karya da cin fuska. Ba littafin tarihi bane da zai amfanar da matasa da masu zuwa nan gaba, sai dai kawai ga ‘yan ta’adda.”
Babangida Ya Sauya Sunansa Domin Ya Hade da Arewa – Vatsa
Jonathan Vatsa ya kalubalanci asalin Babangida, yana mai cewa tsohon shugaban ya sauya sunansa daga Badamosi zuwa Babangida domin ya danganta kansa da yankin Arewa.
“Mutanen Arewa ba sa daukar sunan Badamosi; wannan suna yana da alaka da mutanen Kudu maso Yamma,” in ji shi.
Karya Kan Soke Zaben June 12
Tsohon sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya yi ikirarin cewa Babangida yana kokarin gujewa laifinsa a batun soke zaben June 12.
“Ta yaya zai ce Abacha ne ya soke zaben June 12 alhali shi ne ke rike da mulki a matsayin shugaban kasa?”
Ya kara da cewa:
“Abin takaici ne cewa mutanen da ya zarga da soke zaben sun riga sun mutu, don haka ba za su iya ba da nasu labarin ba. Wannan shine dalilin da yasa ba wanda zai dauki wannan littafi da muhimmanci.”
“Har Yanzu IBB Na Cin Zarafin Vatsa da Iyalan Sa”
Vatsa ya koka da cewa har yanzu, bayan rasuwar marigayi Janar Vatsa, Babangida bai bar shi da iyalansa su huta ba.
“Har yanzu IBB yana cin zarafin mamaci da iyalansa. Ai an ga karshen ɗan’uwanmu, amma Babangida bai san yadda zai kare nasa ba.”
Ya bayyana farin cikin iyalan Vatsa cewa yadda jama’a suka mayar da martani kan wannan littafi yana nuna cewa kisan Janar Vatsa an yi shi ne saboda kishin-kai, hassada da kyashi.
A T P Hausa
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ