Babban Birnin Tarayya Kammala koyawa almajirai 120 Sana’o’in Hannu

Alfijr

Alfijr ta rawaito hukumar gudanarwar ta babban Birnin Tarayya Abuja, FCT, ta hannun sakatariyar cigaban al’umma , ta kammala shirin yaye ‘Almajirai’ sama da 120 da su ka samu horon sana’o’i daban-daban.

Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya, Abuja, Dakta Ramatu Aliyu ce ta bayyana hakan a wata ziyarar gani-da-ido ta yau da kullum a sakatariyar da aka saba yi, a yau Talata a Abuja.

Alfijr

Almajiran dai an zaɓo su ne daga manyan titunan Abuja, inda aka yi musu gyaran hali da rayuwa a cibiyar koyar da sana’o’i ta FCT Bwari.

Ramatu ta ce horon wani ɓangare ne na matakan aiwatar da dabaru a wani fanni na tabbatar da alkawarin da shugaban kasa Buhari ya yi na fitar da ƴan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci nan da shekaru 10 masu zuwa.

Alfijr

Ministar ta bayyana gamsuwa kan abin da ta bayyana a matsayin ‘babban sauyi’ na masu rauni a cikin al’umma.

Ta sake yabawa shirin da ma’aikatan gudanarwa na sakatariyar da suka yi kan yadda shugaban kasa ya samar da ayyukan yi.

Sai dai ta umurce su da su kara yawan matasa a cikin shirin horaswar da nufin cimma ƙudirin na shugaban ƙasa.

Alfijr

Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa

Slide Up
x