Dubun Wani Matsafi Da Ya Kwakwalewa Wani Yaro Idanu A Jihar Bauchi Ta Cika.

Alfijr
Alfijr ta rawaito rundunar ƴan Sandan jihar sun kama Ibrahim tare da kwayar idanun Uzairu guda biyu da ya cire kamar yadda kuka gani

kwanaki biyu da suka wuce an kawo labarin wani yaro matashi Uzairu Salisu a cikin garin Bauchi wanda wani matsafi mai suna Ibrahim ya yaudareshi da niyyar zai bashi kwadago ya kaishi gonarsa ya daureshi ya kwakwule masa idanu guda biyu ya gudu da su

Alfijr

Yanzu haka Uzairu ya fara samun sauki sakamakon kula da lafiyarsa da ake a Asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa University Teaching Hospital Bauchi

Kamar yadda Rariya suka wallafa