Babbar Magana! Gwamnatin Tarayya Tayi Barazanar Daure Shugabannin Kananan Hukumomi

IMG 20240525 WA0104

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta yi barazanar gurfanar da shugabannin kananan hukumomi da kansilolin da aka samu da hannu wajen yin amfani da kudaden da aka ware na asusun bai daya na kananan hukumomi wato Federation Account Allocation Committee (FAAC).

Alfijir labarai ta ruwaito babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), Fagbemi (SAN), ya bayyana hakan a ganawar sa da manema labarai a ranar Alhamis.

Idan zaku iya tunawa dai kotun koli ta yanke hukuncin ne a ranar 11 ga watan Yuli, inda ta ce daga yanzu gwamnatin tarayya ta biya kudaden kason kananan hukumomi kai tsaye daga asusun tarayya.

Kotun kolin ta kuma umarci gwamnatin tarayya da ta hana kason kananan hukumomin da ba zababbu ba da gwamnan ya nada.

Fagbemi, a wajen taron shekara-shekara na shekara 17 na kungiyar Marubuta Kare Hakkokin Dan Adam ta Najeriya da aka gudanar a Abuja, ya ce babu daya daga cikin shugabannin da ke da kariya kuma za a daure shi idan ya yi kaca-kaca da kudaden da ake son bunkasa yankunansu.

“Amma abin da ya bambanta shi ne: kar ku manta, gwamnoni suna da kariya, shugabannin kananan hukumomi ko kansiloli, ba su da wani kariya, don haka sai su zabi tsakanin mu’amala da kudaden kananan hukumomin yadda suke so da kuma kasadar tafiyar su zuwa kurkuku. Zabin sune.

“Idan har suna son karkatar da wadannan kudade to su shirya tunkarar shiga gidan yari, zabin su ne. Idan suna son rubuta sunayensu da haruffan zinariya, dole ne a mayar da ayyukan kamar gine-gine ko gyaran hanyoyi ga karamar hukumar. Ba sai sun zo Abuja ba.

“Idan suka ci gaba da zama a kananan hukumomin su, za mu iya samun raguwar matsalar tsaro da muke fama da shi a Najeriya a yau.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *