Wata babbar kotun Jihar Kano, ta sanya ranar 20 ga watan Nuwamba, domin cigaba da sauraren kararrakin da aka shigar akan Shugaban Jam’iyyar APC na Ć™asa Dakata Abdullahi Umar Ganduje da wasu mutane 7 na cin hanci da rashawa a yau Laraba.
Alfijir labarai ta rawaito gwamnatin jihar ta gabatar da tuhume-tuhume takwas da suka haÉ—a da zargin karbar rashawa, da almubazzaranci da kuma raba kuÉ—aÉ—en Gwamnati a tsakaninsu da suka kai biliyoyin Nairori akan Ganduje, tare da matarsa, Hafsat Umar.
Sauran wadanda ake tuhumar sun haÉ—a da Abubakar Bawuro, da Umar Abdullahi Umar, da Jibrilla Muhammad, da Lamash Properties Limited, da Safari Textiles Limited da kuma Lasage General Enterprises Limited.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj