Badakala! Kotu Ta Ƙwace N1.5bn Daga Tsohon Shugaban NIRSAL.

IMG 20240221 102833

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace Naira biliyan 1.58 da ake alakantawa da tsohon Manajan Darakta na Hukumar ba da Rancen Noma (NIRSAL), Aliyu Abatti Abdulhameed.

Alfijir labarai ta rawaito Mai shari’a Inyang Ekwo ya umarci Hukumar EFCC wadda ke karar tsohon shugaban na NIRSAL ta da wallafa umarnin a jarida, domin jin ko akwai wani mai hujjar da za ta hana kotun ba da umarnin dindindin na kwace kuɗaɗen, cikin kwanaki 14.

Alkalin ya ba da umarnin nen bayan EFCC ta gurfanar da Abdulhameed da Dokta Steve Olusegun Ogidan da mukarrabansu kan haramtattun kudaden da hukumar ta kwato daga hannunsu.
Lauyan EFCC, GI Ndhe Esq, wanda ya gabatar da bukatar, ya ce kotun ta bayar da umarnin damka wa gwamnatin tarayyar kuɗi Naira biliyan 1,582 da aka samu wadanda ake zargi sun same su ne ta haramtacciyar hanya.

A ƙarshe alkalin ya dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 20 ga watan Maris.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *