Daga Aminu Bala Madobi
Asusun Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Dr Attahiru Bafarawa Foundation ya zakulo wasu mutane da za.su rattara bukatocin al’ummar Jihar Sokoto, musamman mabukata, kwamitin wanda Sadaukin Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki ke jagoranta tare da wasu mambobin daga gaukacin kananan hukumomin jihar da mambobin babban kwamitin.
Alfijir Labarai ta rawaito tsohon gwamnan Sokoto Alh Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ba da biliyan É—aya ga mutanen jihar Sakoto domin rage masu raÉ—aÉ—in talauci da suke ciki.
Tsohon Gwamna Bafarawa ya yi bayanin ne a wurin ƙaddamar da Gidauniyarsa da za ta raba kuɗin ga mabuƙata a ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar Zakka da waƙafi na jiha Injiniya Muhammad Lawal Maidoki, a gidansa ranar Laraba data gabata, ya yi godiya kan damar da mutanen Sakkwato suka ba shi kan haka zai ci-gaba da hidimta masu har abada.
“A shekarun da na shafe a matsayin gwamna na yi Æ™oÆ™ari wajen ganin an samu gajiyar dimukuradiyya ga al’umma, gwamnatina ta samu nasara wajen aiyukkan raya kasa musamman shimfiÉ—a hanyoyi da inganta kiyon lafiya da raya ilmi, hakan ya sa na tabbatar da an yi amfani da dukiyar Sakkwatawa yanda Yakamata.
“Idan na tuna soyayyar da Sakkwatawa suka nuna min sai na so na wuce abin da na yi a yanzu, la’akari da yanda aka tafiyar da gwamnati ana iya samun kuskure hakan ke sa akwai bukatar kawo irin wannan sauyi don samun rabo a wurin Allah, abin da ya bani azama na rama alheri da Sakkwatawa suka yi min ba tare da la’akari da duk wani alheri dana yi a lokacin da nake gwamna.
“Alaka ta da Sakkwatawa ba zan taÉ“a mantawa da ita ba shekaru 17 bayan na sauka Gwamna ina murna da farin cikin ganin al’umma ba ta sauya ba, zamana dan shekara 70 da haihuwa burina na cika duk wani giÉ“i da aka samu a dangantaka ta da al’umma. Wasu za su kira wannan a matsayin neman afuwa amma na fi son a dubi rama alheri ne da alheri na soyayyar da aka nuna min kuma yanzu ne yafi da cewa a lokacin da jama’a ke cikin halin matsi hakan ya sa na fitar da kudi naira biliyan É—aya don ganin an samar da jin dadi da walwalar Sakkwatawa,” kalaman Bafarawa kenan.
Ya juya kan kwamitin da ya samar ya ce shugaban kwamitin ya amince da rikon amanar sa kuma sananne ne a wurin gudanar da irin wadannan aiyukkan, Jinkan Alummah da yiwa Addini Hidima, shirin tallafin zai zagaye dukkan ƙananan hukumomin Sakkwato, za a mayar da hankali wurin samar da abinci ruwan sha da sutura ga mutanen jiha.
Ana sa ran mambobin kwamitocin na kananin hukumomin za su tattaro bukatocin kananin hukumomin zuwa ga babban kwamitin jiha don samun saukin ayukka.
Shugaban Kwamitin, wanda shine shugaban Kungiyar Zakka da wakafi na kasa ya bayyana cewa kofar su bude take dan karbar shawarwarin yadda za a samun nasarar aikin, ya bukaci addu’ar al’ummah dan samun nasarar shirin.
Rariya
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj