Bisa ga sahalewar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ana sanar da daukacin masu rike da mukaman gwamnati da suka sauka daga kan mukaman nasu domin yin takara a zaben Kananan Hukumomi da ke karatowa, amma hakan bata samu ba, kuma suke da sha’awar komawa kan mukamin nasu.
To a yanzu haka zasu iya zuwa ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, wato Cabinet Office, daga ranar Talata, 24 ga watan Satumba, shekara ta 2024 domin cike takardun da suka kamata.
Sanarwa daga:
Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida:
Baba Halilu Dantiye, MON, mni.
21/9/2024
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj