Matsalata a Majalisar Dattawa ta fara ne lokacin da na ki yarda da tayin lalata na Akpabio, in ji Natasha Akpoti, inji yar majalisa Natasha.
Natasha Akpoti-Uduaghan, Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, ta yi zargin cewa matsalarta a Majalisar Dattawa ta fara ne bayan ta ki yarda da tayin lalata daga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Akpoti-Uduaghan ta yi wannan zargin ne yayin wata hira da Arise TV a ranar Juma’a.
“Matsalata kamar ta ɗaliba ce da ake hukunta ta saboda ta ki yarda ta kwanta da malamin ta,” in ji ta.
Wannan batu ya jawo cece-kuce, inda ƙungiyar kare haƙƙin mata ta Voices for Inclusion and Equity for Women (VIEW) ta yi Allah wadai da yadda Akpabio ya yi wa Akpoti-Uduaghan.
A wata sanarwa da suka fitar, ƙungiyar ta bayyana wannan lamari a matsayin wani ɓangare na tsangwama ga mata a siyasar Najeriya da ya zama dole a bincika kuma a kalubalanta.
A gefe guda, wasu shugabannin yankin Kudu maso Kudu sun musanta rahotannin da ke cewa akwai rashin jituwa tsakanin Akpabio da Akpoti-Uduaghan, suna mai cewa dangantakar su tana nan lafiya lau. Sun bayyana zargin cin zarafi da wariya a matsayin “mugunta kuma rashin kirki.”
Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa daga ofishin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan waɗannan zarge-zargen.
Walkiya
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ