Bankin Duniya ya gargaɗi Nijeriya kan janye sabbin manufofin tattalin arziki da gwamnati ta kirkiro

IMG 20241017 175230

Bankin duniya ya bukaci gwamnatin tarayya da kada ta sauya manufofin da aka bullo da su na gyaran tattalin arziki, yana mai gargadin cewa hakan na iya haifar da mummunan tasiri ga kasar.

Kawar da tallafin man fetur da kuma soke tsarin musayar kudaden waje ne manufofin da  gwamnati mai ci ne ta bullo da su a rana ta farko da hawan ta mulki.

A yayin da gwamnatin tarayya ta ke kare manufofin, da dama daga cikin ‘yan Najeriya na kokawa da irin tasirin da suke da shi ga talakawa.

Da ya ke jawabi a wajen kaddamar da rahoton ci gaban Najeriya (NDU) a Abuja a yau Alhamis, daraktan bankin duniya a Najeriya, Dr. Ndiame Diop, ya ce duk da cewa sauye-sauyen na iya kawo wahalhalu, sun zama dole domin daidaito kan tattalin arziki.

Diop ya yi gargadin cewa, “Mayar da wadannan sauye-sauyen zai yi illa kuma babbar matsala ce ga Najeriya.”

A nashi bangaren, Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na ci gaba da bijiro da manufofi da ta ke yi.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *