Bayan sanarwar da shugaban hukumar zabe ta jihar Kano Farfesa Malumfashi yayi na rage kudin fom din takarar zaben kananan hukumomi baya ta haihu.
Alfijir Labarai ta rawaito Barasta Hassan Tanko Kyaure ya ce maganar rage kudin Fom da Farfesa Malumfashi yayi shifcin Gizo ne babu alamar kamshin gaskiya cikinsa.
Kyaure ya kara da cewar maganar da Farfesa yayi ta cewar sun rage kudin fom bisa umarnin da kotu ta bayar na karar da jam’iyyu guda uku suka shigar, wannan abu ya bamu mamaki a matsayinsa na Farfesa mai daraja.
“Don haka nake kira ga Jama’a da su yi watsi da wannan maganar tasa, domin babu kamshin gaskiya cikinta.”
Barasta ya kara da cewar, odar da kotu ta bayar a gaban mai shari’a Emeka Unweke na babbar kotun tarayya, cewa tayi, ta dakatar da hukumar zabe ta jihar Kano karbar Naira miliyan 10 daga dan takarar ciyaman, su kuma kansiloli miliyan 5, har sai ta gama sauraron shariar, zuwa 25th ga watan Satumba din nan 2024.
Don haka muke jan kunnen jam’iyyu kar wanda ya yarda da wannan zancen har ya bashi kudinsa! Na sha mamaki a matsayi irin na Farfesa ya dinga irin kokarin shirya zance da sunan kotu, domin ya karbi kudaden jama’a.



Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj