Alfijr
Alfijr ta rawaito autan Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, wato Mustapha Ado Bayero a ranar lahadin data gabata 19 ga Yuni 2023, ya auri mata biyu, inda aka daura masa aure da mataye biyu lokaci daya 11 na safe, daya a kan titin sabuwar Jami ar Bayero ta Kano. Dayan kuma a garin tsakuwa duk a kano
Mustapha Ado Bayero, shi ne dan Auta a cikin Yaya 63 wanda mai Martaba marigayin Sarkin Kano ke da su.
Alfijr
Mustapha dan Sarkin Kano Marigayi Alhaji Ado Bayero, kani ne ga mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Allah Ya Ba Su Zaman Lafiya Da Zuri’a Dayyaba!