Alfijr
Alfijr ta rawaito maikatan NAFDAC hukumar dake kula da tabbatar da ingancin abinci da magunguna a Najeriya sun tsunduma yajin aiki.
Sun tsunduma yajin aikin nasu ne sakamakon yadda suka koka kan ƙin biyan su albashi.
Alfijr
Ma’aikatan wadanda ke karkashin kungiyar maikatan lafiya MHWUN, sun sanar da tsunduma yajin aikin yau Laraba.
Shugaban kungiyar Auwalu Yusuf Kiyawa, ke jawabi a jihar Lagos, ya ce yajin aikin ya fara daga yau.
Alfijr
Auwalu Kiyawa ya kara da cewa kungiyar bazata janye yajin aikin ba har sai an biya ƴaƴanta hakokin su.