Bikin Bude Daso Event Center A Kano

 Yadda Jaruma Saratu Gidado Daso Ta Bude Katafaren Gidan Biki.

Jarumar tayi Matukar kokari wajen Samar Da Katafaren Gidan Bikin a birnin kano,, sannan tayi godiya ga Allah daya bata ikon Samar Da wajen, sannan tayi godiya ga wadanda suka dafa Mata wajen Aikin gini tun daga Farko  Har karshe, masu kula da wajen da kuma wadanda suka bada shawarwari Har aka kai Ga Nasarar Budewa. 

Isma il Afakallah shine Shugaban Hukumar tace Fina finai da Dab I, Kuma Karkashin Hukumarsa ake bada izinin Bude duk wani gidan Biki ko Walima a jihar kano, Shima ya Sami halartar taron Kuma ya yaba da sanya albarka. 

Fasihin Mawaki Nura M Inuwa Shima ya Sami Halartar Bude gidan bikin ya Kuma Rera Wakoki don nishadantar da mahalarta taron. 

Mun sake gano shahararren Mawakin nan Dauda kahutu RARARA a wajen taron, Inda Shima ya rewa waka da sanya albarka. 

Rukayya Dawayya itama na daya daga cikin mahalarta wannan taron, domin kowa yasan ta hannun Daman Daso ce. 

Jarumi Nura Mado Tare Da shugaban Hukumar tace Fina finai Kenan a wajen bikin. 

Aisha Humaira matshiyar Jaruma ita ma ba a Barta a baya ba wajen Taya Daso murnar Bude wannan Katafaren wajen Bikin. 

Jerin ma aikatan wannan kanfanin Dano Event Center Kenan suma suke taya Uwar gidan nasu murna

Jaruman Kannywood Irinsu Baballe Hayatu, Yakubu Muhd, Umar Gwambe, Hadizan Saima da Sauran Manyan jarumai da Kananan wadanda Sai a Vedio Zaku gansu sun Sami halartar. 

Sunshine Decoration 

Shine kamfanin daya Samar Da duk Kwalliya da kayan Kawa da kuka gani a wajen wannan taron na Daso Event Center, Karkashin Jagorancin Sulaiman. 

Don haka kaima ko kema idan Kuna son bikin ku yayi dai dai da wannan ko Yafi wannan, kwa Iya Neman Sunshine Decoration ko ku nemi wannan jaridar ta hadaku dashi. 

Gidan Biki Daga M C Mal Ibrahim Shafukan. 

Wannan kamfani ya Shahara Wajen kayatar daku da karawa bikinku Armashi da karsahi, sune suka kawo kayan Sauti da kayan Nishadi wajen taro. 

M c Mal Ibrahim Sharukan dai Babban M c ne a kasar nan Shima, don haka Ga duk Mai son bikinsa ya zama abin kwatance a ko Ina kake a kasar nan da Fadin duniyar Hausawa kwa Iya nemansa Shima. 

Daso Event Center dai an Bude shine a birnin Kano karamar Hukumar Kumbotso unguwar Yankusa. 

Sauran Karin bayanin suna cikin vedio dake kasa, kwaji daga bakin Mai gayya Mai aiki Haj Saratu Daso. 

Duk shagalin Bikin yana ciki Vedio din.

Allah ya sanya alkhairi yasa an Bude a Sa a ameen ameen. 

Vedio Daso Event

Slide Up
x