YAN KABILAR IGBO NA NEMAN DA A YAFEWA Nnamdi Kanu

Zan Yi Nazari Sosai Kan Sakin Mazi Nnamdi Kanu- Inji Shugaba Muhammadu Buhari. 

Da safiya Juma a ne Jagororin Al ummar Ibo suka kaiwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wata ziyara. 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai yi nazari na neman a saki Nnamdi Kanu wadda ƙungiyar dattawan al’ummar Ibo suka gabatar masa.

Nnamdi Kanu wanda ake zargi da aikata ta’addanci a gaban kotu, na hannun ‘yan sandan farin kaya na DSS sakamakon gwagwarmayar da yake yi ta neman kafa ƙasar Biafra a kudancin Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da aka haramta.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin dattawan a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama Mbazulike Amaechi.

“Kun nemi abu mai matuƙar girma a wajena a matsayina na shugaban wannan ƙasa. Tasirin buƙatar taku na da girma sosai,” a cewar Buhari cikin wata sanarwa da Femi Adesina ya fitar, kamar yadda BBC ta wallafa.

Ya ƙara da cewa buƙatar da dattijan suka nema “ta saɓa wa tanadin tsarin mulki da ya fayyace tsarin shugabanci tsakanin gwamnati da ɓangaren shari’a”.

“Sai dai buƙatar da kuka gabatar mai girma ce sosai amma zan yi nazari a kanta,” in ji Shugaba Muhammadu Buhari 

Slide Up
x