Bincike: Lakurawa ne suka dasa bom a Zamfara – Yan sanda

IMG 20241007 WA0012

Rundunar Yan sandan Zamfara ta tabbatar da mayaƙan Lakurawa ne suka dasa bom ɗin da ya halaka matafiya a yankin Ɗansadau dake Jihar.

Rahotanni sun tabbatar da sau biyu bama-baman ɗin da ake zargin ’yan ta’adda ne suka dasa suka fashe, Majiyar ta ce wata motar haya da ke tafiya a ƙauyen ’Yar Tasha a kan hanyar zuwa yankin Ɗansadau a safiyar ranar Laraba.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalijan, ya tabbatar da harin ga mamema labarai amma ya ce mutum guda ne ya rasu, a yayin da wasu uku suka samu raunuka bayan motar ta bi ta kan abin fashewan da aka dasa a ƙarƙashin wata gada.

Dalijan ya ce, “binciken farko ya gano cewa Lakurawa ne suka dasa bom ɗin. Yanzu so suke su tsere daga Zamfara zuwa Birnin Gwari saboda takura musu da jami’an tsaro suka yi.”

Tinubu yazo ne domin ya cece Nigeria, in ji memban majalisar wakilai
Memba na Majalisar Wakilai daga mazabar Yagba, Hon Leke Abejide, a ranar Laraba ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda zai canza Najeriya. Abejide, mamba daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya kara da cewa Tinubu zai fitar da kasa daga cikin mawuyacin hali.

Daily Post

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *