Gaisuwa Mai tarin yawa da Albarka a gare k ya dawainiyar rayuwa da fama da jagorancin Al umma musamman Yan kwankwasiyya.
Na rubuto maka wannan Wasika ne a matsayina na dan Kano, Musulmi kuma mai nazari da bibiyar al’amuran rayuwa da cigaban al’umma da kishin kasa da kuma abubuwan dake faruwa tsakaninka da dan gidan ka wato Excellency Eng. Abba Kabir Yusuf.
Ina so in maka tuni da cewa shi shugabanci da shekaru suna da kalubale masu tarin yawa wanda daga ciki akwai hakuri, juriya , Kau da Kai, lallashi, cizawa da kuma hurawa, Lallai shugaba sai yayi kokari ya jure.
A matsayinka na shugaba kuma dan kusan shekara 70, babu abunda baka gani ba sai kadan, duba da gwagwarmaya da kayi da damarmakin da ka samu wasu ka nemo da kanka wasu aka nema maka ko aka maka alfarma ka samu haka, kaima ka yiwa wasu alfarma.kuma bai zama dole ka samu abunda kake so a kowane lokaci ba, idan ka dage sai ka samu, to wannan na iya haifar maka da matsala kamar yadda ka Sani.
Duk daɗin zama akan iya samun sabani a tsakani, amma wannan baya nufin sai an fito kan titi ana ta yamadidi da sabanin, Saboda wasu abubuwan bana kan titin bane, kuma duba da shekaru da dadewar da akayi tare ga surukuntaka a tsakani, Ina ganin kame wa shine abunda zai fi zama maslaha da Alkhairi.
Ina so in tuna maka rigimar da ta faru tsakaninka da sahibinka Dr Abdullahi Umar Ganduje, Irin hasarar da ta jawowa Jihar Kano, da kaskanci, wulakanci, tozarci da asarar dukiya da Koma baya da rabuwar kan mutane a Addini, siyasa , Kasuwanci , Zumunci da zamnantakewa mara misali, kuma har yanzu da sauranta, yanzu kuma aka sake kunno wata sabuwa kar, ai wannan ba zai haifar mana da mai ido ba.
Mun yi hasashen rigimarnan za ta murkushe kudade sama da trillion goma in zaa sata a ma’aunin tattalin Arziki, wanda shine abunda nake dalibta akai, don haka ya kamata a kiyaye. Ba ma bukatar wani sabon rikici a jiharmu don Allah…!!!!
Kun zauna sama da shekara 30 da Gwamna kuma anyi abubuwa na kyautatawa juna da sirruka wanda Allah ne kawai ya Sani, to yanzu bai kamata ka bari ana fadawa surikinka kuma dangidanka maganganu ba har ma da Allah ya Isa a gabanka aka yi masa baka ce komai ba. Kuma Kai da kanka a matsayinka na Jagora kake ta fadar maganganu akan Gwamna Wanda ba Irin tsarkake shi da ba kayi ba a baya.
Yanzu maganar ka ta farko Jama a zasu dauka akan Gwamna ko wacce kake yi yanzu..???
Kwankwaso ka fini Sanin cewa , Siyasa ra’ayi ce, kuma zabi ne da yanci na dan’adam, kuma babu abokin tafiya na dindindin haka babu abokin hamayya na dindindin sai dai buqata ta dindindin, don bai kamata a samu hatsaniya ba, don an samu sabanin bukatar, musamman ma da yake ba yau farau ba, domin a harkarnan an samu irin wannan tsakanin uba da dansa a democradiyyar Nigeria ko a turai, don haka abi a hankali don Allah.
Mutane da yawa suna bada shaidar Irin biyayyar da Abba yake maka cewa da Wahala ‘yayan da ka haifa ma su maka irinta, domin ai ana ganin su kuma baa ga suna maka yadda Abban yake maka ba duk da su ba gwamnoni bane. Ya kamata ko don wannan ka kame bakinka kuma kaja girman da Allah ya baka.
Mai girma Jagora kada ka bari tarin mabiya yasa ka dinga tunanin kamar kai ba ka kuskure, ko kai kadai ne ka iya komai, wanda kai da kanka kasan ba gaskiya bane. Jagora kayi kuskure da dama a rayuwarka musamman Kai da kayi aikin gwamnati kuma kayi shugabanci kuma zaka iya yin kuskure a gaba, don haka bai kamata a dauki kuskuren wani a dinga talla da shi kamar akan sa aka fara ba. Kuma idan akace za’a bibiyi abubuwan da kayi a Gwamnati, zai yi wahala ba’a samu kurakurenka ba a matsayin ka na ɗan Adam, don haka a jawa mabiya kunnen a zauna lafiya.
Jagora wannan zai zama abun kunya da gori idan aka cigaba da hura wutar sabanin nan a gareka da shi Gwamnan ga wadanda suke hamayya da kai da magauta da yan kidanka na jiyo da yan bani na iya da sauransu, sabida akwai wasu da yawa da suke so suyi amfani da wannan damar suci zarafinka ko shi gwamna Abba to kun bude musu kofa kenan.
Akwai kuma mutane a qasarnan masu ganin girmanka da daraja da mutuncinka, wallahi duk zasu daina idan haka ta ci gaba.
Haba jagora kai da kake neman shugabancin Nigeria, mai ya kaika tsaya wa local derby, ai kamata yayi ka mai da hankali wajen hada kan abokan tafiya na ciki da wajen kasarnan da tsare tsaren cigaban kasa, da yadda za’a gudanar da mulkin idan an samu , matsalolin da za’a fuskanta na yanzu da na gaba masu zuwa, da nuna capacity, tenacity , knowledge and technical know-how, experience and exposer.
Amma yanzu da Irin wadannan abubuwa ai wasu zasu ce ka kasa managing Kano Wanda jiha daya ce aikin 36 a Nigeria, ta yaya zasu zabe ka ko a mataimakin shugaban kasa?.
Hakazalika zargi ya yi yawa cewa kai kake tafiyar da Gwamnatin Abba, ko don wannan ai ya kamata ka dan kauce ka bashi damarsa ya gwada basirarsa kamar yadda da kanka ka tabbatar, daga Nan ne Kai ma zaka yi free daga duk Irin wadannan zarge zargen, kuma ka samawa kanka salama don gaskiya wannan zai fi maka alkhairi ni a fahimtata.
Don Allah a daina zancen cin Amana da Butulci akan wannan lamarin, domin abubuwan nan da ake zargin Abba yayi sun faru da dama a siyasance, Wanda Kai ma baka kubuta daga su ba, duk wanda yasan tarihi yasan haka. Sai dai kuma idan zaka amsa cewa Kaima cin amanar kayi da butulcin a baya. Gwara a barshi ko kirashi da sabanin fahimta faqat. Wannan zai rage fushi da tunzura magoya baya na bangarorin biyu.
A karshe, ga shawarwarina kamar haka:
1. Don Allah ka rage yawan magana domin Annabi sallallahu alaihi wa Salam yace , “duk Wanda yayi shiru , to ya tsira”. Kuma shi gwamna har yanzu Bai ce komai ba.
2. Idan da hali, ka tattara ka bar Kano a yanzu sai an kwana biyu ka dawo.
3. A hana magoya baya magana ba wuccin gadi
4. Ka Koma kan National politics
5. Ka cigaba da hada kan magoya bayanka.
6. Akwai masu rubutun tsokana da cin zarafi a hana su suma.
7. A yafe wa juna koda da sabanin fahimta don za’a iya haduwa a wata bukatar.
8. In ta kama za’ayi jawabin, to a kyutata harshe musamman a gaban Yara…
Daga karshe nake cewa, na yi wannnan rubutun ne ba don na Isa ba, ko wata manufa ba, sai don Abunda Musulunci yayi umarni kuma a matsayina na da, kuma makocin ka wanda kuma muka yi tafiya daya a baya don Neman maslaha da cigaban al’umma.
Ma’assalam,
Com. Sani Bala Tela.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t