Shugaban Nigeria ya Bada Umarnin ta baci Kan Yan Ta adda kasar nan
Shugabu Muhammadu Buhari ya bawa manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin fatattakar ƴan bindigar da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma na wasu sassan ƙasar.
BBC ta ruwaito ministan harkokin cikin gida na ƙasar Rauf Aregbesola yana sanar da hakan a yau Alhamis bayan taron majalisar tsaro ta tarayya wanda shugaban ƙasar ya jagoranta a fadarsa.
Ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya Bawa duk kannin jami’an tsaron ƙasar umarni da kada su yi ƙasa a gwiwa su tabbatar sun kawar da duk wasu ɓarayi da masu garkuwa da mutane da duk wasu nau’uka na laifuka.
Hanyar Abuja zuwa Kaduna dai ta zama tamkar tarkon mutuwa ganin yadda ake yawan samun ƴan bindigan na yi wa matafiya kwantar ɓauna.
Allah ya kawo mana Karshen wannan masifar a kasar nan ameen summa ameen.