Shugaba Buhari Ya Amince Da Rabawa Mata Rishon Girki Kyauta a kasar Nan

 Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Amince da Raba Mata Kyautar Rishon Girki kyauta a kasar nan

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na raba wa matan aure rishon girki a duk fadin kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar Nigeria.


Ministan Harkokin Mata, Pauline Tallen ce ta sanar da hakan ranar Laraba yayin kaddamar da taron kwanaki hudu wanda Hukumar Makamashi ta Kasa (ECN) ta shirya domin fadakar da mata a kan hatsarin da ke tattare da amfani da itace wajen girke-girke.


Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, an kaddamar da taron ne a kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na rage matsalolin da ke tattare da yawan amfani da itacen girki ga Mata a kasar nan.

Ministar ta yi wa Shugaba Muhammadu Buhari godiya da ya amince a raba rishon girki guda 1000 a kowace karamar hukuma da ke fadin kasar.

Ministar ta Kara da Cewar Shugaba Buhari ya yi la’akari da hatsarin da mata ke fuskanta da yawan wadanda ke mutuwa duk shekara saboda shakar hayakin itace wajen girke-girke.

Ministan ta Kara da cewar, hakan zai kuma taka rawar gani a fafutikar da mahukunta ke yi wajen magance matsalar sauyin yanayi da ake fama da ita a nan gida Najeriya da sauran sassa na duniya.


Allah ya taimaki kasarmu Nigeria ya Kara mana lafiya da zaman lafiya ameen. 


Ana iya tuna cewa, a watan da ya gabata ne Karamar Ministar Mahalli, Sharon Ikeazor, ta ce fiye da mata da kananan yara 90,000 ne ke mutuwa duk shekar a sanadiyar shakar hayakin itacen girki.