Cin Amana! Kotu Ta Tisa Keyar Wani Hadimin Tsohon Gwamnan Gidan Gyaran Hali.

IMG 20240202 194808

Kotun Majistare ta Yaba, a ranar Litinin, ta bayar da umarnin tsare wani Victor Abayomi, mai dafa abinci ga tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, bisa zargin satar wasu kayayyaki masu daraja ta miliyoyin Naira a gidan tsohon gwamnan na Ikoyi.

Alfijir labarai ta rawaito babbban Alkalin Kotun, Mista Peter Nwaka, ya bayar da umarnin tsare wanda ake kara na tsawon kwanaki 30 a gidan gyaran hali na Ikoyi.

Abayomi yana fuskantar tuhume-tuhume guda biyu da suka shafi hada baki da kuma sata da hukumar tsaro ta jihar ke bincikensa da su.

Lauyan da ke shigar da kara na hukumar DSS, Joshua Babalola, ya shaida wa kotun cewa Abayomi da sauran wadanda har yanzu ba a san su ba sun hada baki a tsakaninsu inda suka aikata laifukan a gidan tsohon gwamnan.

Ya yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya kwashe wasu abubuwa masu daraja na miliyoyin naira daga gidan mai gidansa da ke Ikoyi.

Babalola ya ce wanda ake zargin ya gudu ne zuwa Old Garage, karamar hukumar Molorundo, jihar Osun, inda aka kama shi a ranar 7 ga Maris, 2024.

A cewar mai gabatar da kara, laifukan sun ci karo da sashe na 287 da 411 na dokar laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.

Sai dai Alkalin Kotun Mai shari’a Nwaka ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 8 ga Afrilu, 2024, domin gudanar da bincike tare da bayyana gaskiyar lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *