Cin Hanci! ICPC Ta Sami Nasarar Kwato Kadarori Na Sama Da Naira Biliyan 450

Screenshot 20240307 203151 com.android.chrome edit 2597043297520

Daga Aminu Bala Madobi

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ICPC ta jihohin Kano da Jigawa, Ibrahim Garba Kagara, ya bukaci kafafen yada labarai da su bada hadin kai yadda ya kamata wajen ba da rahoton ayyukan hukumar ke gudanarwa.

Alfijir labarai ta rawaito a yayin gangamin taron yini guda don horar da ‘yan jarida da aka gudanar a birnin Kano, kwamishinan ya jaddada babbar manufar shirin na yin mu’amala da ‘yan jarida tare da tunatar da su muhimmiyar rawar da suke takawa wajen bincike da bin kwakkwafin rahoto kan cin hanci da rashawa, wanda ke kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin kasa.

Kagara ya jaddada cewa hukumar na hadin gwiwa da ‘yan jaridu domin zabirar dasu muhimmancin sanar da jama’a illar cin hanci da rashawa, yana mai cewa, “Muna son shigo da ‘yan jarida a bangaren mu domin samun nasarar ayyukan hukumar.

Mista Kagara ya kara da cewa, babu wata hukuma ita kadai da za ta iya yaki da cin hanci da rashawa ba tare da hadin kai daga daidaikun mutane, kungiyoyi da hukumomi da ma sauran kafafen yada labarai ba.

Ya kuma yi kira ga ‘yan jarida da sauran al’umma da su rika tattaunawa da hukumar cikin hikima domin samun bayanan ayyukan cin hanci da rashawa, ta hanyar yanar gizo ko ofishinsu a jihar.

A jawaban da ya gabatar, mataimakin kwamishinan hukumar a jihar, Mista Hassan Salihu kuma kwararren Dan jarida, ya jaddada nasarorin da hukumar ta samu daga shekarar 2019 zuwa 2022, da suka hada da binciken shari’o’i 4,705 da aka kammala, da shigar da kararraki 309 a kotuna daban-daban, da kuma gurfanar da wasu kararraki 387 a kotuna daban-daban.

Bugu da kari, hukumar ta ICPC ta kama tare da kwato kaya ko kadarori masu daraja sama da Naira biliyan 450 a cikin wa’adin shekaru uku dasuka gabata.

Shugaban Sashen Ayyuka, Mista Abubakar Jibrin, ya yi karin haske kan aikin hukumar ke gudanarwa tareda yin tsokaci gameda irin nasarorin da hukumar ta samu a kokarin inganta ayyukanta.

A nasa jawaban da ya gabatar, Femi Gold Babban jami’in labarai na hukumar, ya bayyana muhimmancin da rawar da kafafen labarai ke takawa wajen yaki da cin hanci da rashawa da dai sauransu.

‘Yan jarida daga kungiyoyin yada labarai daban-daban da suka hada da na bugawa, yada labarai, da kuma kafafen yada labarai na yanar gizo a fadin jihar ne suka halarci gangamin taron.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *