Shugaban Najeriya Tinubu Ya Nada Abba Ganduje Mukami

FB IMG 1709852110537


Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada Engr Umar Abdullahi Umar Ganduje (Abba Ganduje) mikamin
Babban Daraktan aiyukan Fasaha na hukumar samar da wutar lantarki a karkara ta Kasa.

Umar Abdullahi Umar dai wanda aka fi sani da Abba Ganduje da ne ga shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Shugaba Tinubu ya dakatar da shuwagabannin hukumar samar da wutar lantarki a yankunan karkara ta Nigeria bisa zarge zargen almundahana.

Wadanda aka nada din dai sun hadar da

(1) Abba Abubakar Aliyu – Manajan Darakta/CEO

(2) Ayoade Gboyega – Babban Darakta, Ayyukan Kamfanoni

(3) Umar Abdullahi Umar – Babban Darakta, Ayyukan Fasaha

(4) Doris Uboh – Babban Darakta, Asusun Lantarki a Karkara (REF)

(5) Olufemi Akinyelure – Shugaban Sashen Gudanar da Ayyukan Lantarki na Najeriya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *