Ana tuhumar mahaifiyar yarinyar nan mai shekara shida da ta ɓata a Afirka ta Kudu da laifi fatauci da garkuwa da diyarta.
Alfijir labarai ta rawaito an gabatar da wannan tuhuma ne a kan Kelly Smith tare da saurayinta da wasu mutane biyu a shari’ar da ta ba da mamaki a kasar.
Joslin Smith ta ɓata a wajen gidansu da ke kusa da birnin Cape Town a ranar 19 ga watan Fabarairu.
Bincike ya gano rigarta da jini a jiki, amma ba a ga yarinyar ba, duk da binciken da aka ƙaddamar na hadin-gwiwa da sojojin sama da jirage marasa matuka da karnuka.
Kafin wannan lokaci mahaifiyar yarinya ta ce ba za ta saduda ba har sai an gano diyarta ta a raye.
A cikin kowanne sa’a biyar ana samun rahotannin ɓatan yara a Afirka ta Kudu.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk