Civil Defence Sun Damke Wani Tsoho Mai Shekaru 85 Bisa Zargin Yin Garkuwa Da Yaro A Kano

Screenshot 20240308 114208 com.android.chrome edit 3133585038583

Jami’an hukumar tsaron Civil Defense reshen karamar hukumar Ungoggo a kano, sun samu nasarar cafke wani tsoho mai suna Ibarhim Usman mai shekaru 85 a duniya bisa zarginsa da aikata laifin garkuwa da wani karamin yaro mai shekaru 3 a Duniya wanda dan makocinsa ne domin karbar kudin fansa.

Alfijir labarai ta rawaito kakakin hukumar tsaron civil defense na jahar  Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan ta cikin Wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai a ranar Alhamis.

Ya ce mutumin yayi garkuwa da Yaron ne a Unguwar Rimin Kebe dake karamar hukumar Ungogo, inda yake kokarin boye yaron a Hotoro a gidan wani abokinsa.

Rahotanni na cewa, Wanda ake zargin ya yaudari yaron ne da Alewa har ya dauko shi a cikin baburin Adaidaita sahu, sai dai Abokin nasa yaki karbar yaron.

Bayan haka Abokin nasa ya tafi da yaron zuwa Unguwar Rimin Kebe, kuma ya samu dandazon jama’a suna ta kokarin ganin yadda za a samu Yaron.

Koda a watanni biyu da suka gabata dattijon da ake zargi ya taba Karbar nambar mahaifin Yaron, amma bai taba kiransa ba.

Wasu dai sun shaidawa hukumomin tsaron cewar an ga dattijon da yaron, amma dai ya musanta zargin.

A karshe kakakin hukumar tsaron civil defense din Ibrahim Idris ya ce yanzu haka sun fara fadada bincike kan lamarin kuma da zarar an kammala za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *