Da Ɗumi Ɗuminsa! An Kama Shugaban Karamar Hukuma Da Laifin Kashe Matarsa

Alfijr ta rawaito rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Nnewi ta Arewa Mbazulike Iloka kan mutuwar matarsa.

Alfijr Labarai

Kakakin rundunar ‘yan sandan Anambra, Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar haka ga manema labarai.

Ya ce rundunar ta hannun hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (SCID) tana ci gaba da gudanar da bincike domin sanin hakikanin abin da ya faru.

Tochukwu ya ce an kama shi ne bisa zargin cewa yana da alaka da mutuwar matarsa, Chidiebere a makon jiya.

An dakatar da shi nan take lamarin da Gwamna Chukwuma Soludo ya bada umarnin hakan

Alfijr Labarai

Ana zargin tsohon Shugaban, wanda aka fi sani da Mba, da kashe matarsa a wani rikicin cikin gida, zargin da ya musanta, inda ya ce ta fadi ta mutu ne kawai

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam g Campiagn for Democracy (CD) da Human Rights Liberty Access and Peace Defenders Foundation (HURIDE) sun kai karar babban sufeton ‘yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba da ya kama tsohon shugaban domin ya zama darasi ga wasu.

Alfijr Labarai

An ce Chidiebere ta mutu ne a ranar 7 ga Agusta, 2022 bayan ta yi wa mijinta karin kumallo, amma majiyoyi sun ce mutuwarta ba ta dace ba yadda mijin nata ya bayyanar ba

Slide Up
x