Da Ɗumi Ɗuminsa! Kotu Ta Yanke Hukuncin kisa kan Wanda Ya Kashe Hanifa Abubakar

Alfijr

Alfijr ta rawaito Wata babbar kotu a jihar Kano da ke a Najeriya ta yanke hukuncin kisa akan Abdulmalik Tanko kan samun sa da laifin kashe Hanifa Abubakar., dalibarsa

Alkali Usman Na’abba ne ya yanke hukuncin a yau Alhamis 28 ga watan Yulin 2022.

An gurfanar Abdulmalik Tanko ne bisa zargin sace Dalibarsa Hanifa mai shekara 5, tun watan Disambar 2021 tare da kasheta ya binne a gidansa.

Alfijr

Kotun ta sami Abdulmalik Tanko da laifin garkuwa da Haneefa, da laifin kisa.

Kotun ta sami Hashimu Isyaku da laifin hada kai wajen garkuwa da kashe daliba Hanifa.

Kotu kuma ta wanke Fatima Jibril daga zargin rubuta wa iyayen Hanifa wasikar sanar da su an yi garkuwa da ita, amma ta same ta da laifin hannu waje yin garkuwa da Hanifa, da masaniyar an yi garkuwa da ita.

Kotu ta daure Fatima shekera biyu babu zabin tara

Slide Up
x