Hukumar DSS ta kama Shugaban karamar Birni Fa izu Dana Gwale Khalid Dana Gwarzo Kutama.

Alfijr ta rawaito jami’an tsaro na farin kaya DSS reshen jihar Kano sun kama Faizu Alfindiki shugaban karamar hukumar Kano, da Khalid Ishaq Diso shugaban karamar hukumar Gwale da kuma Injiniya Bashir Kutama shugaban karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano bisa zargin ‘yan daba.

Rahotanni sun bayyana cewa a baya-bayan nan ne aka kashe kimanin Mutane uku a yayin gudanar da harkokin siyasar Gwamna Ganduje a wasu kananan hukumomin jihar, lamarin da ke barazana ga zaman lafiyar Kano da ta samu a shekarun baya.

Wani babban jami’in DSS da ba ya son a buga sunan sa, ya ce sun kama Faizu Alfindiki Shugaban Karamar Hukumar Kano da Bashir Abdullahi Kutama Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, bisa zargin daukar nauyin ‘yan damfarar siyasa a Jihar, wanda har ya kai ga hare-hare da kashe-kashen da suka biyo baya.

Alfijr

Hukumar ta SS ta kuma sanya Khalid Ishaq Diso shugaban karamar hukumar Gwale ta Kano a kan wannan zargi, yayin da wani Dokta Sabiu SSA ga Gwamnan shi ma jami’an tsaro sun kama shi kan wannan zargi.

Hukumar DSS da ta fusata kan rikicin ‘Yan bangan Siyasa da ke ta karuwa a Kano, wanda ya haifar da kashe-kashe, ta yi gargadin cewa duk wanda aka samu da saka hannun sa ba zai tsira ba.

Alfijr

Wani kazamin fada tsakanin magoya bayan wasu ‘yan takarar siyasa daban-daban a yankin Garo da Burkun na kananan hukumomin Kabo da Bunkure ya yi sanadiyar kashe mutane hudu a kwanan baya.

Babban jami’in DSS din ya bayyana cewa, sun shiga wani gagarumin yunkuri na dakile tashe-tashen hankulan da ke fargabar kona Kano tun kafin a fara zaben 2023 da ya dace.

Slide Up
x