Kotu Ta Daure Kaka Zaliha Isa Dake Unguwar Chiranchi Shekaru 16 A Kano

Alfijr


Alfijr ta rawaito mai shari’a
Amina Adamu Aliyu dake kotu mai lamba 10 Miller Road a kano ta daure Wata mata mai suna Kaka Zaliha Isa ɗaurin shekaru 16 da tarar dubu 20,000

Alfijr

An gurfanar da Kaka Zaliha ne a yau Alhamis 3rd Maris 2022 bisa zargin dauke wata yarinya mai shekara 3, yar makotansu, da sakata a rijiya da niyyar kasheta.

Da farko dai Kaka Zaliha Isa mazauniyar Chiranchi da ke birnin Kano, ta dauke yarinyar ne ta kulle ta a gidanta cikin wani daki mai duhu, daga bisani ta sakata a wani bokiti ta tsundumata a rijiya.

Alfijr

An yi ta neman yarinyar har kwana biyu ba a ganta ba.

Bayan kwana 2 ne, Kaka Zaliha ta nemo mai yasar Rijiya da ya yashe mata rijiyar da zummar ta gani ko yarinyar ta mutu, mai aikin na shiga sai yayi karo da wannan yarinyar a bokiti, daga nan ya fito yaje ya shaidawa mai unguwa da sauran mutanen unguwar aka dauko yarinyar da ranta.

Nan dai aka kaita ga jami an tsaro don fadada bincike akan wannan al amari.

Alfijr

Bayan gurfanar da ita a gaban mai shari’a Amina Adamu Aliyu, lauyoyin gwamnati sun gabatar da shaidunsu na tabbatar da cewar Kaka Zaliha itace da hakkin wannan danyen aikin.

Itama wadda ake zargin lauyoyinta sun kawo nasu shaidun don kariya ga Kaka Zaliha Isa.

Alfijr

Ana bangaren Mai shari’a ta gamsu da shaidun da lauyoyin gwamnati na tabbatar da laifin Kaka Zaliha Isa, sannan tayi watsi da shaidun lauyoyin wadda ake zargi.

Da take yanke hukunci kan laifukan da ake zargin Kaka Zaliha dasu na hadin kai wajen ɗauke yarinya yar shekara 3, sai laifin garkuwa da tayi da yarinya, sai laifi na 3 yunkurin kisan kai.

Alfijr

Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta daure Kaka Zaliha shekara 2 a laifin hadin dai wajen sace yarinya.

Sai daurin shekaru 7 bisa laifin garkuwa da tayi da yarinya da kuma tarar kudi dubu 20,000

Sai kuma laifi na 3 ɗaurin shekaru 7, bisa yunkurin kisan kai da tayi niyyar yi.

Alfijr

Da take karin bayani akan laifin kisan kai, mai shari’a tace laifin hukuncinsa daurin rai da rai ne ko kuma mai shari’a na da zabin kasa da haka bisa adalci, wannan dalili yasa ta daure kaka shekaru 7 bisa wannan laifin.

Ta kuma kara da cewa hukuncin zai fara ne tun daga lokacin da aka kama wadda ake tuhuma.