Alfijr ta rawaito jarumar Kannywood, Fati Usman wacce aka fi sani da Fati Slow Motion tayi bayani kan yadda aka kai karshen takkadama da ya faru a Kannywood kwanakin baya a tattaunawarta da BBC Hausa cikin shirin daga bakin mai ita.
Alfijr
An tambayi Fati Slow game da yadda aka yi aka kawo karshen dambarwar da ya faru kwanakin baya, sai ta ce:
Fati Slow ta bayyana cewa masana’antar fim ta yi masu uwa ta yi masu uba shiyasa ta fito ta yi magana tun farko don kareta.
Ta bayyana cewa komai ya zo karshe ne bayan Naziru sarkin waka ya tsamo ta daga yanayi na kebura da take karba wato (talauci) domin, sai da ya cire min kebura 99 daga jikinta.
Alfijr
Ta kuma yi kira ga al’ummar Annabi da su dinga taimakawa mutane, ta hakan ne lamarin zai daidaita a wannan yanayi da ake ciki na bakin talauci.
Fati Slow ta bayyana cewa mutane na yawan yi mata gori kan rashin yin aure yaushe Zaki yi aure, ni kuma na dauka kamar da mutuwa da aure kamar duk lokaci ne.
Alfijr
“Na san cewar Allah bai manta da ni ba, koma menene na san Allah bai manta da ni ba. Idan Allah ya yi zan yi aure kafin in mutu zan yi, idan Allah ya yi ba zan yi aure ba zan koma ga rabbi-ssamawati ban yi aure ba toh wallahi babu wanda ya isa ya daura mun aure. Alkawari ne na Ubangiji sai lokacin da ya cika shi.”
Da aka tambaye ta game da amsar da take bayarwa idan aka yi mata tambayar, jarumar ta ce:
Alfijr
“Dama amsa ce kwaya biyu. Ka san ranar da za ka mutu? Idan kace mun baka san ranar da za ka mutu ba, toh shikenan magana ya kare.”