Da Ɗumi Ɗuminsa: Daga Ƙarshe Hukumar DSS Ta Kama Emefiele

Alfijr ta rawaito Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tabbatar da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele a hannun ta.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya ya fitar kuma Alfijr Labarai ta samu a yau Asabar.

A cewarsa: “Hukumar DSS a nan ta tabbatar da cewa Mista Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) yana hannun ta saboda wasu dalilai na bincike.

An umurci jama’a, musamman kafafen yada labarai, da su yi taka-tsan-tsan a cikin rahotanni da kuma labaran da suka shafi hakan.

“Ƙarin bayani da za a biyo baya….

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *