Gwamnatin Kano Ta Ci Gaba Da Rushe Gine-Ginen Da Ta Ce An Yi Ba Bisa Ka’ida Ba

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin jihar Kano ta cigaba da rushe gine-ginen da akai ba bisa ka’ida ba.

An rushe gine-ginen da ke filin wasa na Sani Abacha, da wadanda ke GSS Kofar Nasarawa kusa da titin IBB da kuma wadanda ke GGSS Dukawuya a Goron Dutse.

Tawagar Gwamnan sun ci gaba da rusau din ne a yau Lahadi da safe, wanda hukumar KNUPDA ta jagoranta.

Idon zaku iya tunawa tsohon gwamnan jihar ta Kano Abdullahi Ganduje ya kai karar Sanata Rabiu Kwankwaso gurin Tinubu domin ya dakatar da rusau din da Gwamnatin NNPP take a Kano.

Haka zakilika shima Sanata Kwankwaso a nasa bangaren ya shaidawa yan jaridun fadar shugaban kasa cewa Tinubu ya kadu mutuka da ya shaida masa barnan da gwamnatin Ganduje tayi a Kano.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

3 Replies to “Gwamnatin Kano Ta Ci Gaba Da Rushe Gine-Ginen Da Ta Ce An Yi Ba Bisa Ka’ida Ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *