Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ayyana dokar ta-baci a faɗin yankin Yammacin Afirka, sakamakon ƙalubalen tsaro da juyin mulki da ke ƙaruwa a wasu ƙasashen mambobinta.
Wannan mataki na zuwa ne a matsayin martani ga hauhawar barazanar tsaro, musamman juyin mulki a wasu ƙasashe, da kuma yunƙurin dawo da tsarin dimokuraɗiyya da zaman lafiya a yankin.
A cewar shugabannin ECOWAS, wannan dokar ta-baci za ta bai wa ƙungiyar damar ɗaukar matakan gaggawa don kare dimokuraɗiyya, samar da zaman lafiya da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Za a ci gaba da bibiyar wannan mataki don ganin yadda zai shafi kasashen yankin.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t