Alfijr ta rawaito Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fita zuwa magariba a jihar Kano, ta sanya dokar ta-baci da nufin kaucewa karya doka da oda, sakamakon tashe-tashen hankula da suka biyo bayan tattara sakamakon zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Litinin.

Ya ce an yanke shawarar ne don hana ’yan daba su haifar da hargitsi a cikin halin da ake ciki.

Kwamishinan ya yi kira ga jama’ar jihar da su kasance a cikin gida domin jami’an tsaro ba za su kyale kowa ko kungiyar da ke da niyyar haddasa fitina ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Ubanku ya ci uwatai. Lokacin da kukayi naku wa yayi magana. Alhamdulillah ALA ni’imatika alay