Da Dumi Duminsa! Gwamnatin Jihar Kano ta kori wasu ma’aikata Daga Bakin Aikinsu

Gwamnatin jihar Kano ta kori wasu ma’aikatan gwamnati hudu da aka kama da takardun bogi

Best Seller Channel 

Gwamnatin jihar Kano ta kori wasu ma’aikatan gwamnati hudu da aka kama da takardun bogi da bayanan karya. 

KANO FOCUS ta rawaito cewa hukumar ta kuma amince da karin girma ga ma’aikata 126 a cikin manyan ma’aikatan gwamnati. 

Best Seller Channel 

Shugaban Hukumar Bello Mohammad Kiru ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis jim kadan bayan kammala taron koli na yau da kullun na manyan ma’aikata da ake gudanatwa a dakin taro na hukumar. 

Sanarwar da Daraktan wayar da kan jama’a ta CSC, Ismail Garba Gwammaja ya aike wa KANO FOCUS wadanda aka karawa girman sun hada da mataimakan daraktoci biyar a mataki na 15 da aka kara masa girma zuwa mataki na 16 a matsayin Daraktoci, 36 a mataki na 14 da aka daukaka zuwa matsayin mataimakan daraktoci a mataki na 15. yayin da sauran su ne na tsakiya da manyan jami ai. 

Kiru ya bayyana jin dadinsa bisa yadda aka gudanar da atisayen cikin sauki sannan kuma ya bukaci ma’aikatan jihar da su ci gaba da ba hadin kai ga wannan gwamnati domin a gaggauta amincewa da karin girma ba tare da tsangwama ba.